An Kama Mataimakin Gwamnan Kano, Kwamishina

Dr. Abdullahi Umar Ganduje gwamnan Kano

‘Yan sandan Kano, sun kama mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Nasiru Yusuf Gawuna da kwamishinan kananan hukumomi, Murtala Sule Garo, sanadiyyar zarginsu da aka yi da laifin haifar da hatsaniya a ofishin tattara sakamakon zabe da ke karamar hukumar Nasarawa.

Baya ga haka, an kama shugaban karamar hukumar ta Nasarawa.

Hakan na faruwa ne yayin da ake harhada hancin sakamakon zabukan kananan hukumomin jihar 44 bayan zaben gwamnoni da na ‘yan majalisun jihohi da aka yi a ranar Asabar.

Wasu hotunan bidiyo da ke ta yawo a kafofin sada zumunta, sun nuna cewa, ana zargin mutanen ne da laifin kokarin lalata takardun da suke dauke da sakamakon zaben karamar hukumar ta Nasarawa.

Ya zuwa lokacin faruwar wannan lamari, an kammala kidaya sakamakon zaben hukumomi 43 saura na karamar hukumar Nasarawa.

Kuma kamar yadda bayanai da rahotanni ke nunawa, jam’iyyar PDP mai adawa a jihar ta Kano, ita ke gaba da yawan kuri'u.

Ya zuwa lokacin hada wannan rahoto, mutanen uku na tsare a ofishin ‘yan sanda da ke yankin Bompai, kamar yadda bayanai suke nunawa.