An Kama Sojojin Da Su Ka Yi Yinkurin Juyin Mulki A Gabon

  • Ibrahim Garba

Laftana Obiang Kelly lokacin da ya ke karanta jawabin juyin mulkin

Yayin da Shugaba Ali Bongo na Gabon ke jinya a kasar Moroko (Morocco) sanadiyyar bugun zuciya, sojojin kasar sun yi yinkurin yi masa juyin mulki amma ba su yi nasara ba.

Wani mai magana da yawun gwamnatin Gabon ya ce an damke dukkannin manyan hafsoshin sojan da su ka yi yinkurin juyin mulki da safiyau yau din nan Litini, inbanda guda.

"An kama hudu ana kuma neman dayan," a cewar mai magana da yawun gwamnatin Gabon Guy-Bertrand Mapangou.

Jami'an soji sun kwace Gidan Rediyo Na Kasa mallakin Gwamnatin Gabon, a yau dinnan Litini a Libreville babban birnin kasar.

Sojojin sun bayyana niyyarsu ta kafa abin da su ka kira majalisar sake farfado da kasa.

Laftana Kelly Ondo Obiang ya bayyana ta gidan rediyo, cewa jawabin da Shugaba Ali Bongo ya yi ta gidan rediyo kwanan nan, a ta bakinsa, "ya dada kawo shakku kan ko shin Shugaban zai iya cigaba da gudanar da ayyukansa yadda ya kamata."

Shugaba Ali dai na kasar Morocco, inda ya ke cigaba da murmurewa daga bugun zuciya.