An Kama ‘Yan Kasuwar Da Suka Sayar Da Abin Sha Mai Guba A Kano

  • Murtala Sanyinna

Hukumar kula da sahihancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC

Hukumar kula da sahihancin abinci da magunguna ta Najeriya, NAFDAC, ta cafke ‘yan kasuwar da ke da alhakin sayar da abinci da kayan sha da ke kunshe da miyagun sinadirai, da suka yi sanadiyyar mutuwar wasu mutane a Kano.

Mutum 3 ne ake hasashen sun mutu sanadiyyar shan wasu nau’o’i na abin sha a jihar Kano a cikin watan Maris, wadanda binciken farko ya nuna suna kunshe da sinadirai masu guba da lahani ga lafiyar dan adam.

Wata sanarwa da kakakin hukumar Olusayo Akintola ya fitar, ta ce hukumar ta sami nasarar kama ‘yan kasuwar da ke da hannu a sayar da kayayyakin, duk da yake dai ba’a bayyana sunaye ko adadin mutanen da aka kama ba.

Farfesa Mojisola Adeyeye, Shugabar Hukumar NAFDAC

Sanarwar ta ce shugabar hukumar ta NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye ta yi gargadi akan yin karin sinadirai ga abinci da ababen sha domin karin dandano, tana mai cewa hakan kan iya haifar da mummunan rashin lafiya da kuma mutuwa.

Karin bayani akan: NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, jihar Kano, Nigeria, da Najeriya.

Adeyeye ta ce “hukumar ba za ta yi saku-saku ba, wajen tabbatar da inganci da sahihancin abinci da magunguna da ake sayarwa jama’a a kasuwanni.”

Ta ce tuni hukumar ta aike da sakamakon binciken farko da ta yi akan wadanda lamarin ya rutsa da su a Kano, zuwa ga gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, a lokacin ziyarar da ta kai ta kwana 2 a jihar sakamakon al’amarin.

Abdullahi Umar Ganduje, Gwamnan Jihar Kano

Ta ce babbar nasara ce da aka samu kama ‘yan kasuwar da suka kawo abin shan mai dauke da munanan sidadirai, wanda hakan zai ba da damar fadada bincike da daukar matakan da suka dace.