An Kammala Taron Kasa-da-Kasa Kan Zaman Lafiya A Birnin London

Mata suna saye da sayarwa a kasuwa

Kwamishinan al'adu da hadin kan addinai na jihar Bauchi ya bayyana zaman lafiya a matsayin kashin bayan dukan rayuwar al'umma ba tare da nuna banbancin addini, yanki, kabila ko kasa ba.
A karshen makon da ya shige ne aka kammala taron kungiyar hadin kan addinai da zaman lafiya ta Duniya a birnin London Kasar Britaniya.

Taron ya hada kai wakilai dabam dabam daga kasashen duniya da suka hada da wakilai daga nijeriya

Wakilimmu a London Mohammed sani Dauda,wanda ya halarci taron ya kuma gana da wasu daga cikin 'yan tawagar Nijeriya, ya ruwaito cewa, kungiyar karfafa zumunci da zaman lafiya a tsakanin addinai dabam dabam na duniya wanda aka fi sani da kungiyar UPF ta shirya a bana, ya sami wakilci mahalarta da dama daga nahiyar Afrika.

Kwamishinan raya addinai da hadin kan al’umma na jihar Bauchi Alhaji Salisu Ahmed Barau yana cikin tawagar Najeriya da suka halarci taron ya kuma bayyana muhimmancin taron da abinda suka koya.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Kwamishinan Jihar Bauchi Alhaji Salisu Ahmed Barau-3:58