An Kashe Musulmi 'Yan Kabilar Rohingya Da Dama - MDD

  • Ibrahim Garba

Wasu jama'a da ke kyautata zaton 'yan kabilar Rohingya ne yayin da wani kwalekwale ya sauke su a gabar ruwan kasar Malaysia

Wasu mazauna kauyen Buthidaung sun ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na soji ne ya kai hari kan wani gungun ‘yan Rohingya, wadanda ke tara itacen gora a ranar Alhamis.

Ofishin da ke kula da ‘yancin dan adam a Majalisar Dinkin Duniya, ya ce akwai fargabar yiwuwar an kashe dunbin Musulmi ‘yan kabilar Rohingya.

An halaka mutanen ne a wani hari da jirgin sama mai saukar ungulu na sojojin Myanmar ya kai a makon jiya, sabanin adadin mutune bakwai da aka ce tun farko.

Mai magana da yawun Babban Kwamishina Mai Kula Da Harkokin ‘yancin dan adam a Majalisar Dinkin Duniya, Ravina Shamdasani ta ce, “Yanzu mu na samun rahotannin da ke nuna cewa da alamar adadin ya fi haka sosai. Mun samu wasu rahotannin da ba mu tantance ba da ke nuna cewa adadin na iya kai wa 30.”

Wasu mazauna kauyen Buthidaung sun ce wani jirgin sama mai saukar ungulu na soji ne ya kai hari kan wani gungun ‘yan Rohingya, wadanda ke tara itacen gora a ranar Alhamis.