Wannan hari ya faru ne lokacin da aka kai wa wani shingen sojan da ke garin na Mamfe hari a kasar ta Kamaru.
An kai harin ne bayan da wata tawagar Najeriya ta musamman ta tabbatar wa kasar ta Kamaru cewa za su hada hannu domin yaki da ta'addanci a wannan wuri.
Dama kasar ta Kamaru ta jima tana kokawa akan yadda ‘yan awaren suke amfani da bakin iyakar Najeriya a masayin wurin yin atisayensu.
Wakilin wannan gidan radiyon mai aiko da rahotanni daga kasar ta Kamaru, Moki Edwin Kindzeka, ya ce Ministan sadarwa kuma mai Magana da yawun gwamnati Issa Tshiroma ya tabbatar da aukuwar lamarin.
Ya kuma ce dubban matasa ne dauke da makamai da suka hada da bindigogi da adduna, da kwari da baka suka kai wa’yan sandan dake yankin na Mamfe hari
Harin ya auku ne a daren ranar Alhamis din da ta gabata.
Tchiroma ya ce sakamakon haka ne dan sanda guda ya mutu kana 5 daga cikin maharan suma sun mutu, sannan wasu da dama musammam daga cikin maharan suka samu raunuka.