An kashe mutane ashirin da takwas a Iraq suna sallar Tarawih

Wasu jami'an tsaro ne, suke nazarin inda aka kai hari cikin Masalacin Um Al Qura a birnin Bagadaza kasar Iraq.

Wani mai harin kunar bakin wake ya tarwatsa kansa cikin Masalacin 'yan Sunni a birnin Bagadaza ya kashe mutane ashirin da takwas da raunana mutane talatin da bakwai.

Jami'an kasar Iraq sunce wani mai harin kunar bakin wake ya tarwats akansa cikin Masalacin yan Sunni a birnin Bagadaza ana Sallar Tarawih, ya kashe mutane ashirin da takwas da raunana mutane talatin da bakwai.

Jami'an ma'aikatar harkokin cikin gidan Iraq, sunce a jiya Lahadi da dare wannan al'amari ya faru a cikin Masalacin Um Al Qura a Bagadaza baban birnin kasar. Sun baiyana cewa wani dan Majalisar wakilan kasar mai suna, Khalid Al Fahdawi dan Sunni wanda ke wakiltar mazarbar lardin Anbar a yammaci kasar yana daga cikin wadanda aka kashe.

Babu dai wata kungiyar data fito nan da nan, tayi ikirarin cewa ita keda alhakin kai wannan hari, da aka kai ana dab da kare azumin watan Ramadan. Akalla wasu karin mutum hudu sun mutu a sakamakon wata tarzoma a jiya Lahadi.

Tarzoma ta ragu a Iraq tun shekara ta dubu biyu da shidda da kuma shekara ta dubu biyu da bakwai, to amma kai hare hare abu ne da aka saba gani a kasar. Jami'an Amirka dana Iraq sun baiyana damuwa akan iyawar Iraq wajen tinkarar matakan tsaro bayan sojojin Amirka sun janye daga kasar a karshen wannan shekara.