Accessibility links

Rashin Lantarki da Ambaliyar Ruwa Sun Biyo Bayan Guguwar Irene

  • Halima Djimrao-Kane

Ambaliyar Ruwan da Irene ta haddasa a New York.

Miliyoyin Amurkawa sun yi fama da duhun rashin lantarki da kuma Ambaliyar ruwa bayan Guguwar Teku ta Irene

Miliyoyin mazauna gabar gabashin Amurka sun yi fama da rashin wutar lantarki da kuma ambaliyar ruwa,bayan da karfin mahaukaciyar guguwar teku ta Irene ya ragu, ta danna zuwa kasar Canada.

Hukumomi sun bada rahoton mace-mace 21 a kalla sanadiyar mahaukaciyar guguwar tekun a jahohin gabashin kasar Amurka da dama, inda ta haddasa bannar dubban miliyoyin daloli. Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya fada ranar lahadi cewa za a dauki makonni ko ma fiye da haka wajen share-share da gyara bannar da guguwar ta yi, kuma ya yi alkawari, gwamnatocin jahohi da na kanana hukumomi za su samu tallafin gwamnatin tarayya.

Masana ilimin hasashen yanayi sun fada da jijjifin litinin cewa Irene ta zama hadirin ruwan sama kawai a lokacin da ta isa gabashin kasar Canada, inda ta kaiwa yankin ruwa da iska. A ranar lahadi karfin ta ya ragu daga mahaukaciyar guguwar teku zuwa hadiri kawai, kafin ta ratsa fadin arewa maso gabashin Amurka, amma duk da haka ta hassada gagarumar ambaliyar ruwa a jahohin New Jersey da Vermont.

Ta New York idaniyar guguwar ta biya ta wuce, amma ba ta yiwa birnin wata babbar banna ba. Hukumomin birnin sun dauki wani matakin ba sabun ba ranar asabar a gabannin zuwan guguwar ta Irene,su ka dauki matakin dakatar da zirga-zirgar jiragen karkashin kasa, wanda hakan ya kawo cikas ga miliyoyin mutanen da su ka saba yin amfani da jiragen kasan. Amma jami'an birnin sun ce matakin da su ka dauka ne ya ba su damar sake bude tashoshin jiragen karkashin kasan akan lokaci ranar litinin a tsakiyar lokacin da aka fi bukatar jiragen kasa da safe.

Amma jiragen kasan da ke yin zirga-zirga daga New York zuwa sauran unguwannin bayan gari da kuma akasarin jiragen kasan New Jersey sun ci gaba da dakatar da ayyukan su saboda ambaliyar ruwa.

Kasuwar hada-hadar hannayen jarin New York ta bude akan lokaci ranar litinin.

Ranar Jumma'a Irene ta fara kadawa a Amurka, ta yada zango a jahar North Carolina kafin ta wuce zuwa gabar New England da sauran jahohin da ke wajejen.

XS
SM
MD
LG