An Kashe Wasu Mutane 2 A Bahrain

Hukumomi a kasar Baharain sun zartar da kisa akan wasu mutane biyu, bayan samun su da aikata laifin Ta’addanci.

An kashe wadannan mutanen biyu ne, duk da irin kiraye-kiraye da kungiyoyin kare hakkin bil’adama na kasa-da-kasa suka dinga yi, na kada a aiwatar da kisan.

Wani gidan jaridan Faransa na AFP ne ya wallafa wannan rahoton, da cewar an kashe mutanen biyu ne ta hanyar harbe su da akayi a yau Asabar.

Kungiyoyin sun bayyana sunayen mutane su biyu Ahmad Al-Malali da Ali Al-Arab.

Sun kuma kara da cewar duka mutane biyu ‘yan kasar ta Baharain ne, da aka yanke musu hukunci akan laifin ta’addanci a shekarar da ta gabata.

Haka shima mutum na uku an ruwaito cewar shima an kashe shi a yau Asabar din, wanda laifin shi bashi da alaka da na Al-Malali da Al-Arab.