An Kulla Yarjejeniyar Kare Hakkin 'Yan gudun Hijra a Nijar

Shugaban Jamhuriyar Nijar, Muhammadu Isufu

A Jamhuriyar Nijar kungiyar lauyoyi  da hukumar UNHCR mai kula  da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya, sun cimma wata yarjejeniya  domin samar da kariyar da ta dace ga  ‘yan gudun hijira da masu neman mafakar siyasa, abinda  masu fafukar kare hakkin dan adam su ka ce ya yi dai dai.

Masu lura da al’amura sun ce wannan mataki zai taimaka wajen karfafa dokar da gwamnatin ta Nijar ta riga ta tanada dangane da kare ‘yan gudun hijrar da masu neman mafakar.

A cewar kungiyar lauyoyin ta Nijar, za a ware wasu lauyoyi na musamman wadanda za su lura da wannan yarjejeniya domin kare ‘yan gudun hijrar.

Wani mai fafutukar kare hakkin bil adama a Jamhuriyar ta Nijar, Abdu Alhaji Idi, ya ce wannan mataki da aka dauka ya nuna cewa ana mutunta ‘yan gudun hijra.

Saurari rahoton da wakilin Sashen Hausa na Muryar Amurka Sule Mumuni Barma ya aiko mana daga Yamai:

Your browser doesn’t support HTML5

An Kulla Yarjejeniyar Kare ‘Yan gudun Hijra a Nijar – 2’27”