An Kusa Samun Zaman Lafiya a Kaduna - Kwamiti

Nigeria National Assembly

Shugaban kwamitin Majalisar dattawan Najeriya, sanata Kabiru Gaya, ya bayyana haka ne ga manema labarai bayan ganawa da Gwamnan jihar Nasiru El-Rufai, a gidan Gwamnatin jihar.

Ya kuma ce kwamitin ya tattauna da masu ruwa da tsaki kuma zai ji ta bakin mutanen da rikicin ya shafa.

Sanata Kabiru Gaya, ya kara da cewa a matsayinsa na tsohon Gwamna suna da wasu shawarwari na sirri da za su baiwa Gwamna Nasiru El-Rufai.

Kakakin Gwamnan jihar Kaduna Mr. Samuel Aruwan, ya ce gwamna ya yi wa ‘yan kwamitin bayani daya baya daya na abubuwan da suka afku daga bangaren gwamnatin jihar Kaduna, da kuma matakan tsaron da gwamnatin ke dauka domin shawo kan wannan matsala da ta ki ci ta ki cinyewa.

Your browser doesn’t support HTML5

An Kusa Samun Zaman Lafiya a Kaduna - Kwamiti - 3'14"