An Maido Da Hanyoyin Sadarwar Talho, Yanar Gizo a Kashmir

Yadda dakarun Indiya suka mamaye yankin Kashmir bayan da hukumomin New Delhi suka janye 'yancin cin gashin kai da aka ba yankin

“Cikin shekaru 72 da suka gabata, mun kuduri aniyyar ganin mun zabi makomarmu, saboda haka, muna masu nanata cewa, a ba mu ‘yancinmu.” in ji daya daga cikin jagororin masu zanga zangar.

A yau Asabar, jami’ai a yankin Kashmir, a bangaren da ke karkashi ikon kasar Indiya, sun fara maido da hanyoyin wayar talho a yankin Himalaya.

Tun dai a farkon watan nan, yankin na Kashmir a bangaren na Indiya ya shiga rudani, bayan da hukumomin New Delhi suka tura dubun dubatar dakarunsu, yayin da suka katse layukan talho da na wayoyin salula da ma na yanar gizo, tare da karbe ikon cin gashin-kai da aka ba yankin, wanda mafi aksarin mazaunansa Musulmai ne.

Jami’an tsaron da suka mamaye yankin, sun zauna cikin shirin ko-ta-kwana, yayin da daruruwan mazaunansa suka bazama akan titunan birnin Srinagar, suna zanga zangar adawa da matakin gwamnatin Indiya ta dauka a a karshen makon nan

“Cikin shekaru 72 da suka gabata, mun kuduri aniyyar ganin mun zabi makomarmu, saboda haka, muna masu nanata cewa, a ba mu ‘yancinmu.” in ji daya daga cikin jagororin masu zanga zangar mai suna Hayat.

Shi dai yankin na Kashmir, kasashen Indiya da Pakistan ne suka kasa shi zuwa gida biyu, amma duk da haka, kasashen na ci gaba da ikrarin daukacin yankin mallakinsu ne.

India da Pakistan, wadanda kasashe ne da suka mallaki makaman nukiliya, sun sha tafka yaki akan yankin na Kashmir, tun bayan da suka samun ‘yancin gashin kai daga turawan mulkin mallakan Birtaniya a shekarar 1947.