An sace tsohon minista Ali Munguno a Maiduguri

  • Aliyu Mustapha

Maiduguri, Najeriya

Wasu ‘yan bindiga sun yi awon gaba da tsohon ministan man fetur na Nigeria Dr. Shettima Ali Munguno jim kadan bayanda aka gama sallar jumu’a a Maiduguri.
Yau ne wasu matasa dauke da makamai suka yi awon gaba da tsohon ministan man fetur na Nigeria, Dr. Shettima Ali Munguno jim kadan bayanda aka kamalla sallar jumu’a a daya daga cikin masallatan birnin Maiduguri. Ance ‘yan bindiga din sunzo ne akan kekensu mai kafa ukku, aka yi salla tareda su, sannan suka umurci wadanda ke tareda Dr. Munguno a cikin motar da su fice, kana suka tafi da shi. Ibrahim Garba Ka-Almasih ya zanta da wakilinmu na Maiduguri, Haruna Dauda kan abinda ya faru:

Your browser doesn’t support HTML5

An sace tsohon minista Ali Munguno a Maiduguri - 2:48