WASHINGTON D C —
Rahotanni daga kasar Kenya sun ce wasu ‘yan bindiga sun sace wasu likitocin kasar Cuba su biyu a Mandera, bayan da suka harbe dan sandan da aka dorowa nauyin kare likitocin har lahira.
Jami’an kasar sun ce su na kyautata zaton barayin ‘yan kungiyar al-Shabab ne dake da alaka da kungiyar al-Qaida.
Mandera shine babban birnin yankin Mandera a arewa maso gabashin Kenya, kuma yana kan iyakar Somalia da Kenya.