An Saka Ranar Zabe a Myanmar

[FILE]

Hukumomi a kasar Myanmar, sun sanar da cewa za a gudanar da zaben kasar a ranar takwas ga watan Nuwamba mai zuwa, wanda zabe ne da aka dade ana dakonsa.

A yau Laraba, shugaban hukumar zaben kasar, U Thaung Hlaing, ya tabbatar da hakan ga Sashen Burmanci na Muryar Amurka.

Ana sa ran jam’iyyar adawa ta National League for Democracy, wacce Aung San Suu Kyi ke jagoranta, za ta taka rawar gani yayin gudanar da wannan zabe.

Sai dai, Suu Kyi, ba za ta samu damar tsayawa takararar shugabancin kasar ba, bayan da majalisar dokokin kasar wacce aksarinta mambobinta sojoji ne, ta yi fatali da wani yunkurin yin kwaskwarima ga kundin tsarin mulkin kasar.

Akwai dai yiwuwar a kawo karshen majalisar da a ce, an amince da wannan kwaskwarima.

A yanzu haka, sojojin kasar na da kujeru 25 a majalisar, wanda adadi ne da ke basu damar yi watsi da duk wani abu da basu yi na’ama da shi ba.