An Sake Zanga Zanga Kan Take-Taken Indiya A Kashmir

  • Ibrahim Garba

Mata ma ba a barsu a baya ba a zanga-zangar ta Kashmir

A cigaba da turjiyar da 'yan yankin Kashmir ke nunawa tun bayan da kasar India ta soke 'yancin cin gashin kai na bangaren yankin Kashmir da ke karkashin ikonta, sun sake shiga zanga-zanga.

Dubban mazauna bangaren yankin Kashmir da ke karkashin ikon Pakistan, sun yi gangami jiya Asabar don dada jaddada bukatarsu, ta cewa Indiya ta kawo karshen matakin nan mai cike da takaddama na fatattakar mutane, wanda ta fara daukawa tun watanni biyu da su ka gabata, a bangaren da ke karkashin ikonta a yankin na Kashmnir da ake rikici akai.

Zanga-zangar ta faru ne a ranar da Sanata Chris Van Hollen na Amurka ya iso Pakistan bayan ziyarar da ya kai Indiya, inda aka hana shi izinin zuwa Kashmir gane wa kansa.

Da ya ke jawabi a birnin Multan na gabashin Pakistan, Van Hollen ya yi kira ga gwamnatin Indiya da ta tabbatar ta kare hakkin dan adam, ta maido da hanyoyin sadarwa ta kuma saki fursunonin yaki na yankin da ake takaddama akai.