An Sallami Uwargida Melania Trump Daga Asibiti

Melania Trump

An salami uwargidan shugaban kasar Amurka Melania Trump daga asibiti yau, bayan ‘yan kwanaki da yi mata aikin da ya shafi koda.

Kakakinta Stepanie Grishman ta fada a wata sanarwa cewa, “uwargidan shugaban kasa tana hutawa kuma tana ci gaba da murmurewa”

Grisham ta godewa duban mutane da suka yiwa uwargidan shugaban kasa Melania fatar laheri da kuma wadanda suka kira ta ta wayar tarho ko kuma aika mata da sakkonin email.

Uwargidan shugaban kasar ta koma fadar White House bayan an yi mata aiki a asibitin Walter Reed dake Bethesda jihar Maryland