An Sami Maganin Jinyar Yara Masu Fama Da Kanjamau

Wata karamar yarinya marainiya dake dauke da kwayar cutar HIV.

Masu bincike sun gano cewa akwai maganin da yake da kaifi da yafi amfani wajen jinyar yara dake da kananan yara dake dauke da kwayar cutar HIV sai dai maganin yana da tsadar gaske, kuma ba a samunshi sosai kasashe masu tasowa.

Binciken mai zurfi da aka gudanar ya nuna cewa, maganin efavirenz yafi nevirapine kaifi wajen kwantar da kwayar cutar AIDS. An buga sakamakon zaben da aka gudanar a Boswaana kan sama da kananan yara dari takwas tsakanin ‘yan shekara 3 zuwa 16 a mujjallar kiwon lafiya da ake kira American Medical Association.

Wannan ne karon farko da aka gudanar da binciken a kan magungunan farko da ake amfani dasu wajen jinyar kananan yara.

Sai dai an bayyana cewa ba za a iya ba kananan yara da shekarunsu suka gaza 3 ba.

An yi kiyasin cewa, sama da kananan yara miliyan uku suke dauke da kwayar cutar HIV a duniya, yawancinsu a kasashen nahiyar Afrika.