An Samu Barkewar Masassarar Tsuntsaye A Jihar Filato

Ma'aikatan kiwon lafiyar dabbobi na kone kajin da suka kamu da masassara kafin su binnesu

Tun watan Janairun wannan shekarar ne cutar masassarar tsuntsaye ta bullo a wasu gonakin kaji a jihar Filato.

Kawo yanzu kimanin kaji dubu talatin da takwas ne ma'aikatar gona a jihar Filato ta hallaka.

A cewar jami'in dake kula da cutar masassarar tsuntsaye a jihar Filato Dr. Haruna Ayuba ya zuwa yanzu manyan gonaki takwas ne lamarin ya shafa inda suka kashe kajin suka kuma binnesu kana suka fesa feshin hana yaduwar cutar.

Ma'aikatan sun jawo hankalin masu gonakin da su dinga kula da yadda mutane ke shiga da fita daga gonakinsu domin kiyaye sake yada masu cutar. Da zara sun lura da faruwar wani abu an gargadesu su sanarda ma'aikatar cikin gaggawa.

Shugaban kungiyar masu kiwon kaji ta jihar Mr. John Dafar yace suna fadakar da 'yanuwansu mahimmancin tsafta a gonakinsu. Yace tun shekarar 2015 zuwa yanzu sun yi hasara kaji fiye da miliyan daya. Idan aka kwatanta hasarar da kudi ta fi nera biliyan daya.

Wasu kajin da suka kamu da masassara

A kungiyance sun ba kansu shawara su yiwa gonakinsu inshora domin rage hasara tunda gwamnati bata taimakonsu idan an samu barkewar cutar kaji.

Ga rahoton Zainab Babaji da karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An Samu Barkewar Masassarar Tsuntsaye A Jihar Filato - 3' 49"