An Samu Karin Mutum 549 Da Suka Harbu Da COVID-19 a Najeriya

Hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Najeriya (NCDC) ta ce adadin wadanda suka kamu da cutar COVID-19 a kasar ya kai 22,614.

Adadin ya kai wanann matakin ne bayan da aka samu karin mutum 594 da suka kamu da cutar a jihohi 22.

Jihohin da aka gano sabbin wadanda suka kamu da cutar sun hada da Lagas inda aka samu mutum 159, 106 a Delta, 44 a Ondo, 34 a Abuja, 34 a Edo, 33 a Oyo, 33 a Kaduna, 28 a Enugu, 25 a Katsina, 22 a Imo, 15 a Adamawa, 12 a Ogun, 11 a Osun.

Sauran jihohin sun hada da Abia mai mutum 8, 6 a Rivers, 5 a Nasarawa, 5 a Bauchi, 5 a Neja, 4 a Kebbi, 3 a Ekiti sai kuma 1 a Plateau da Taraba.

Jihar Legas dai har yanzu ita ce kan gaba ta fannin masu kamu da COVID-19 a Najeriya, yanzu gaba dayan adadinta ya kai 9,482.

Sanarwar da hukumar ta NCDC ta fidda a shafinta na Twitter ranar Alhamis 25 ga watan Yuni ta kuma ce ya zuwa yanzu an sallami mutum 7,822 daga asibiti kana mutum 549 sun mutu.