Hasashen yanayin da da samun ruwa kamar da bakin kwaryaa yawancin sassan Najeriya na zuwa ne bayan fiye da mutum 100 sun riga mu gidan gaskiya a sakamakon ambaliyar ruwa.
Hukumar hasashen yanayin ta baiyana samun wannan ruwa mai cike da tsawa a Alhamis din nan, a wasu sassan kasar kuma an samu gajimare ne.
Shugaban hukumar hasashen yanayin na Najeriya Farfesa Sani Abubakar Mashi ya ce su kan yi amfani da na’urori don gano yanayin yawa ko tsagaitawar ruwan sama. Suna anfani da naurori daban daban su san yaushe za’a yi ruwan da zai yiwa shuka anfani. Y ace yawancin kasashen yammacin Afirka sun dogara ne akan hukumar su domin sanin yanayin damuna.
Mutane dai sun fara fahimtar irin wannan hasashe da yadda ya kan baiyana lokacin shuka ko kawo baraznar ambaliyar ruwa.
Aminu Tangaza manomi ne daga yankin arewa maso yammacin Najeriya da ya ce yanzu su na bin duk lamuran hasashen da hakan kan taimaka mu su wajen daukar matakan da su ka dace. Yanzu mutane kawunansu sun waye. Ana ba da harsashen yanayi ne bisa ilimi ba tsafi ba.
Shugaban hukumar hasashen Farfesa Abubakar Mashi ya aza alhakin samun ruwan saman ba zata kan sauyin yanayi. Y ace abun dake haddasa ruwa a Nigeria wani layi ne inda iska mai kawo zafi da mai kawo ruwa ke haduwa. Duk inda suka hadu dole ne a samu ruwa.
Hukumar hasashen yanayin ta ce ruwa zai dauke cak a watan nan na Satumba a dukkan fadin Nigeria.
A saurari rahoton Nasiru Adamu El-Hikaya
Your browser doesn’t support HTML5
An Samu Ruwan Sama Sosai A Nigeria