An Samu Zaman Lafiya Tsakanin Sojoji Da Fararen Hula a Sudan Ta Kudu

Wasu mazauna garin Wau na kasar Sudan ta Kudu sun ce dangantaka tsakanin sojoji da fararen hula ta ci gaba sosai cikin ‘yan makonnin nan saboda yunkurin samar da zaman lafiya da ake ci gaba da yi.

Dayawa daga cikin fararen hula yanzu sunce basa tsoron ganin wani mai kaki, amma kuma ‘yan kasar sun yi kira ga gwamnati da ta biya sojoji albashinsu akan lokaci ta yadda ba zasu shiga yin wasu abubuwan da basu kamata ba domin samun kudin da zasu ciyar da iyalansu.

Wasu kungiyoyin agaji biyu masu zaman kansu da ake kira Safer World da CEPO masu kula da ci gaban zamantakewar al’umma, sun yi ta shirya tarukan karawa juna sani a garin Wau cikin shekaru biyu da suka gabata, domin farfado da dangantaka tsakanin sojoji da fararen hula.

A wani taron da aka gudanar jiya Talata, akan halin da ake ciki kan dangantakar sojoji da fararen hula a yankin Wau, mazauna yankin sunce lamura sun daidai ta yanzu, kuma yanzu ba wani bakon abu bane aga sojoji da fararen hula kafada da kafada suna sayayya tare da tayin tafiye-tafiye.