An Shiga Rana Ta 31 Da Rufe Wasu Ma’aikatun Gwamnatin Amurka

  • Ibrahim Garba

Ginin Majalisar Dokokin Amurka

Yau Litinin an shiga rana ta 31 da rufe wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka, a yayin da kuma Shugaban Majalisar Dattawa, dan Republican, ke shirya yadda za a kada kuri’a, kan wata shawara da Shugaba Donald Trump ya gabatar ta a daidaita.

Yau Litinin an shiga rana ta 31 da rufe wasu ma’aikatun gwamnatin Amurka, a yayin da kuma Shugaban Majalisar Dattawa dan Republican ke shirya yadda za a kada kuri’a, kan wata shawara da Shugaba Donald Trump ya gabatar ta a daidaita, amma kuma shugabannin Dimokarat ke cewa ba ta ma taso ba.

Tsarin da Trump ya yi tayinsa, ya tanadi kariya ga dubban bakin hauren da aka shigo da su cikin Amurka tun suna kanana, da kuma tsawaita wa’adin kare mutanen da su ka guje ma kasashensu saboda tashin hankali ko wani bala’i. A madadin haka kuma a samar da kudi dala biliyan 5.7 don gina katanga akan iyakar Amurka da Mexico.

‘Yan Dimokarat dai na adawa da batun gina katangar da cewa akwai tsada, gashi kuma ba matakin tsaro ne mai inganci ba. Su na bukatar Trump da ‘yan Republican su bude harkokin gwamnati duka kafin a tattauna kan wasu matakan kare kan iyaka.

Shugaban masu rinjaye na Majalisar Dattawa, dan Republican Mitch McConnell ya ce zai gabatar da tsarin da Trump ya yi tayinsa din, don kada kuri’a a kai.