An Yi Adu’oin Tunawa Da Marigayi Abubakar Tafawa Balewa

Alhaji Sir Abubakar Tafawa Balewa

An gudanar da addu’oin tunawa da Firai Ministan Najeriya n farko, Sir Abubakar Tafawa Balewa, ana ya rasu a wani yunkurin juyin mulki da aka yi shekaru hamsin da daya da suka shige da baiyi nasara ba.

An gudanaqr da adu’oin da ya sami halartar mutane daga kowanne bangaren rayuwa na kasar, a gidan marigayin dake titin kofar rana cikin garin Bauchi,

Wazirin Bauchi Alhaji Waziri Kirba wani dattijo mai kimanin shekaru tamanin da haihuwa, yana daga cikin almajiran marigayi Tafawa Balewa. Ya bayyana cewa, marigayin shine malaminsu na tarihi da turanci bayan dawowarsa daga karatu Ingila. Ya bayyana marigayin a matsayin mai tausayi.

Babban dan marigayi Tafawa Balewa, Baba Abubakar ya bayyana mahaifinsa a matsayin wanda ya sadaukar da kanshi domin yiwa kasa hidima, ya kuma yi aiki domin ganin hadin kan Afrika baki daya da suka zama abin koyi.

Sauran wadanda suka yi jawabai a wajen addu’ar sun yi kira ga sauran al’umma musamman ‘yan arewacin kasar su kasance masu kishin kasa da sadaukar da kai domin yiwa kasa hidima da kuma ganin ci gaba da hadin kan kasa.

Wata kungiya dake hankoron ganin ci gaban Bauchi karkashin jagorancin Zahradeen Baban Tanko ce ta shirya zaman addu’oin.

Ga cikkaken rahoton da wakilinmu Abdulwahab Mohammed ya ya aiko daga Bauchi, Najeriya.

Your browser doesn’t support HTML5

An yi bukin cika shekaru 51 da rasuwar Tafawa Balewa- 3:03