An yi bikin matasa a kasar Kamaru

Shugaban Kamaru, Paul Biya

Ranar 11 ga kowane watan Fabrairu ce ranar da kasar Kamaru ta kebe domin bikin matasa lokacin da shugaban kasa ke yi masu jawabi na musamman.

Kowace ranar goma sha daya ta watan Fabrairu kasar Kamaru tana gudanar da bikin matasa.

Bikin na wannan shekara shi ne karo na hamsin. Shugaban kasar Paul Biya ya yiwa matasa jawabi ta kafafen yada labarai.

A cikin jawabinsa yace duk wani lamarin kasar ya rataya ne akan matasa. Ya jinjinawa matasa wajen dogaro da kai da suka yi na ganin cewa kowa yana kokari ya cimma burinsa na rayuwa. Yace ya sha fada masu kada su ce sai gwamnati ta yi masu komi. Su ma suna iya samar ma kansu ayyukan yi.

Kamaru kasa ce mai cike da arziki saboda haka yace ya san da zamansu domin zasu ci moriyar kasar. A bangaren shugabanci yace zasu yi kokari gaya na tabbatar cewa sun cimma buri na sanya kasar akan turba saboda gobe kowa na iya alfahari da ita.

Yanzu kasar tana kan manya manyan ayyuka na gine-gine saboda a samu kyakyawan sakamako.

A cikin jawabin ya kara ja hankalin matasa su kara karfi da karfe kan aikin noma domin shi ne yake da sauki dake kuma bada anfani. Noma zai kara habaka tattalin arzikin kasar kana matasan na iya dogaro da kansu idan suka rungumi noma musamman idan sun yi shi da ilimin zamani har ma ya basu taimakon kudin sefa miliyan dari da biyu.

Akan tsaro yace sun san kasar na yaki da 'yan ta'adan Boko Haram a arewacin kasar.Ya jajintawa matasan da kokarin kare iayakokin kasar

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

An yi bikin matasa a kasar Kamaru - 5' 06"