An Yi Girgizar Kasa a Jihar California

Yadda wata hanya ta dare biyu bayan girgizar kasar ta California

Cikin kwanakin biyun da suka gabata, wasu girgiza kasa masu karfin gaske sun faru a kudancin jihar California, da ke yammacin Amurka.

Girgizar kasar ta baya-baya nan wacce ta auku a ranar Juma’a, ta kai karfin maki 7.1, ita ce kuma mafi karfin gaske da jihar ta taba gani cikin Shekaru 20, a cewar jami’ai.

hukumomi sun ce a za a ci gaba da jin burbushinta har nan da wasu shekaru masu zuwa.

A cewar Lucy Jones, kwararriya a fannin nazarin yadda girgizar kasa ke aukuwa, karfin girgizar kasar ta ranar Juma’a, ta kai ninkin-baninkin wacce ta abkawa wasu garuruwa a ranar Alhamis.

Rahotanni sun ce dubban mutane a yankin da ake kira Ridgecrest suna zaune babu wutar lantarki.

“An samu raunuka da dama, gidaje biyu sun kama da wuta, wayoyin wuta sun tsittsinke, tankuna iskar gas sun fashe, ire-iren wadannan abubuwan dama su kan faru idan aka yi girgizar kasa.” Inji David Witt, shugaban ma’aikatar kashe gobara a karamar hukumar Kern County a jihar ta California.

Hukumomin sun kara da cewa, an ji jirin girgizar kasar ta ranar Juma’a, har zuwa yankin Sacramento da ke arewa mai nisa, sannan an ji ta har zuwa birnin Las Vegsa da ke can gabashin Amurka da kuma kudancin kasar Mexico.