An Zargi Shugaban Kamfanin Twitter Da Nuna Halin Ko-in-Kula Ga Musulman Rohingya

Jack Dorsey

Shugaban kamfanin Twitter Jack Dorsey na ci gaba da fuskantar suka dangane da halin ko in kula da ya nuna, kan halin matsananciyar rayuwa da Musulmai ‘yan kabilar Rohingya suka shiga, a lokacin wata ziyara da ya kai don sulhu a birnin Myanmar.

Dorsey, ya wallafa a shafinsa na Twitter ranar Lahadi cewar, jama’ar Myanmar na cike da farin ciki, kuma abincinsu yana da dadi.

Masu sukar lamarin, sun ce Dorsey, yayi watsi da irin hallin da mutane sama da 700,000 ‘yan kabilar Rohingya suke ciki, na rasa muhallansu da suka yi bayan da suka yi kaura daga jihar Rakhine da ke arewacin kasar suka koma Bangaladesh da ke makwabtaka da su, sanadiyar wani samame da dakarun Mynamar suka kai kansu, a matsayin martani kan wani hari da wasu mayakan sa kai na Rohingya suka kai kan jami’an tsaron Myanmar.

Masu bincike na musamman na Majalisar Dinkin Duniya sun ce, sojojin sun yi kisan gilla akan ‘yan kabilar ta Rohingya, inda suka ce sun tattaro rahotannin ne daga jama’ar da abin ya shafa, wadanda suka yi zargin an ci zarafinsu ta hanyar kisa da fyade, da kona musu kauyukansu.

A Yau Laraba Dorsey, ya mayar da martani, inda ya ce yana sane da irin halin kuncin rayuwa da mutanen ke ciki, kuma ba da gangan ya ki yin magan akan batun ba.