An Zargi Sojojin Habasha, Kenya Da Cin Zarafin Fararen Hula a Somalia

Sojojin Kasar Kenya Na Kutsawa Cikin Jeji

Kasashen Kenya da Habasha sun yi amfani da karfin soja wanda ya wuce kima akan fararen hular kasar Somalia a daidai lokacin da ake kokarin dakile hare-haren ‘yan kungiyar al-Shabab da ke kai kawo akan iyakar kasashen, a cewar wani rahoto da cibiyoyin agajin dake aiki a Somalia suka fitar.

Rahoton, wanda sashen Somalia na Muryar Amurka ya samu, ya ce Kenya ta kai hare-hare ta sama da dama wadanda suka kaikaici garuruwan da makiyaya ke zaune a yankin Gedo na kasar ta Somaliya tun daga shekarar 2015.

Rahoton ya kuma ce, jami’an dake kula da gobarar daji sun yi ayyukan sintiri na kan iyaka, sun auna mutane, sun kuma yi kamen ganin dama, tare da yin kashe-kashe da dama da ba a hukumance ba.

Rahoton ya kuma ce kasar Habasha ta kai rundunar mayaka wajen iyakar kasar don su kori manoma da makiyayan da suka kafa sansaninsu a wani yanki dake tsakanin Somaliya da kasar Habasha.

Sai dai Kakakin dakarun tsaron Kenya, Kanar Joseph Owuoth ya musanta wadannan zarge-zargen.