WASHINGTON D C —
An ga wasu manyan motoci dauke da fararen hula yau Jumma’a suna fita daga kauyen Baghuz dake gabashin Siriya, tungar mayakan ISIS ta karshe da suka ayyana a matsayin daularsu.
Nan take dai ba a tabbatar da adadin fararen hular da suka rage a kauyen ba dake kusa da iyakar Iraki.
Kamfanin dillancin labaran Associated Press ya bada rahoton cewa wasu motoci samfurin a-kori-kura da aka danawa bindigogi, mallakar dakarun Siriya da Amurka ke marawa baya ne suka raka ayarin motocin fararen hular.
Sabbin hare-haren da aka kai jiya Alhamis, sun auna wajen kauyen Baghuz ne, kwana daya bayan da aka kwashe fararen hula 2,000 daga wurin.