Ana Ta Neman Wadanda Su Ka Bata A Kogin Kwara

ana fargabar cewa mutane da dama sun mutu a cikin hatsarin kwale-kwalen

An tabbatar da mutuwar mutane 70 a kalla a cikin hatsarin kwale-kwalen
Ma'aikatan ceto na ci gaba da neman wasu mutane da dama da suka bata a kogin Kwara bayan kifewar wani babban kwale-kwalen da aka cunkusawa fasinjoji fiye da kima.

Jami'an hukumar ceton gaggawa ta jahar Naija sun fada a jiya asabar cewa an gano gawarwakin mutane da yawa da suka mutu a cikin hatsarin da ya faru tun ranar jumma'a. Wani jami'in hukumar ya ce mutane hamsin ne iyakacin abun da kwale-kwalen zai iya dauka.

Masu gudanar da bincike sun ce a lokacin da hatsarin ya faru kwale-kwalen ya na cike makil da 'yan tireda masu zuwa cin kasuwar mako-mako a garin Malale a daya bangaren kogin.

Kimanin awowi 24 bayan afkuwar hatsarin wakilin Sashen Hausa Murtala Faruk Sanyinna ya samo karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Mutane da dama sun mutu a hatsarin jirgin ruwa a jahar Naija.2':29"