Ana Cigaba Da Gallazawa Bakin Haure A Amurka

Ma’aikatar tsaron cikin gidan Amurka na bincikin wani rahoto, dake cewar wani rukunin ma’aikatan hukumar na yanzu da a da suna cikin masu dabi’ar rubuce-rubuce a shafin Facebook. Inda suke kalaman batanci da nuna tsana da akidar banbancin launin fata akan jinsunan mutane daban-daban.

Binciken da wata kafar labarai da ake kira “ProPublica” ta wallafa ya nuna cewa cin zarafin ya hada da hotunan fyade, da kalamai masu daci da suka shafi mutuwa akan bakin haure, harma da habaici akan wannan mutumin dan kasar El-Salvador wanda ya mutu tare da diyarsa a cikin wani kogi.

Shafin na Facebook ana kiransa da lakabin “I’m 10-15” lambar da ake baiwa bakin haure da suke tsare.

Rahoton ya bayyana yadda ma’aikatan suka bayyana mutuar wani matashi mai shekaru 16 da ya mutu, a matattarar ajiyar bakin haure, da cewa “Ko oho, idan ya mutu, ai ya mutu ne kawai.”