Ana Cigaba Da Tattauna Nukiliyar Iran

[FILE]

Iran da sauran manyan kasashen duniya na ci gaba da tattaunawa a birnin Vienna a yau Laraba, duk da cewa wa’adin da suka shata na gashin-kansu a karo na biyu ya cika.

Yanzu haka wakilan bangarorin biyu sun tsaida ranar Juma’a mai zuwa a matsayin ranar da za a cimma matsaya ta hakika.

A jiya Talata, wani jami’in diplomasiyyar kasar Australia, ya ce tattaunawar da ake da Iran ba ta samar da nasara a kokarin da ake na cimma matsaya ba.

Wani jakadan da ba a bayyana sunan kasarsa ba, ya ce, akwai matukar wahala a gane menene ya sa, ko kuma yadda za a ci gaba da tafiya a haka.

Sai dai wani babban wakilin kasar Iran a wannan tattaunawa, Abbas Araqchi ya ce, babu wani wa’adi da bai sauyuwa, yana mai jaddada cewa, Iran a shirye take ta ci gaba da tattaunawa har illa masha’a, idan har hakan ya zama dole.