Ana Kada Kuri'ar Raba Gardama Kan Sabon Kundin Tsarin Mulki A Zimbabwe

Jama'a sun yi layi a runfunan zabe a kasar Zimbabwe

‘Yan kasar Zimbabwe suna kada kuri’ar raba gardama kan sabon kundin tsarin mulkin kasar, wanda karon farko zai rage karfin ikon shugaban kasa.

Sabon kundin tsarin mulkin zai takaita wa’adin mulkin shugaban kasa zuwa wa’adin mulkin biyu na tsawon shekaru biyar biyar kawai.

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe dan shekaru tamanin da tara, ya shugabanci kasar na tsawon sama da shekaru talatin, kuma ko a karkashin sabon kundin tsarin mulkin ma, zai iya ci gaba da mulki na tsawon shekaru goma.
Mr. Mugabe da abokin hamayyarsa Morgan Tsvangirai, dukansu sun goyi bayan daftarin kundin tsarin mulkin, kuma ana kyautata zaton zai sami gaggarumin goyon baya.

Mutanen biyu sun tsaida yarjejeniyar raba daunin ikon mulkin Zimbabwe bayan kazamin tashin hankalin da ya biyo bayan zaben shekara ta dubu biyu da takwas, sai dai har yanzu suna yiwa juna kallon hadarin kaka. An yi tashin hankali a wurare dabam dabam kafin fara zaben raba gardaman na yau asabar.