Ana Kan Zaben Majalisar Dokoki a Lebanon

  • Ibrahim Garba

Firaministan Lebanon Saad Hariri

Mutanen kasar Lebanon mai fama da takaddamar bangarori na kan kada kuri'a a zaben Majalisar Dokokin kasar.

Yau Lahadi ana zaben Majalisar Dokoki a kasar Lebanon, a karon farko cikin shekaru 9.

A baya an jinkirta zaben sau da yawa saboda yanayin tsaro.

Takarar an fi yinta ne tsakanin gamayyar jam’iyyu da ke karkashin jagorancin Firaminista Saad Hariri da ke samun goyon bayan kasashen yammacin duniya da kuma kungiyar Hezbollah mai samun goyon bayan kasar Iran.

Mata 86 ne ke takarar kujeru a Majalisar Dokokin Lebanon mai kujeru 128, wadda ta rabu daidai tsakanin Musulmi da Kirista.

An girke jami’an tsaro a tasoshin zaben da ake yi yau Lahadi.

Ana kyautata zaton sai bayan wasu ‘yan kwanaki a samu sakamakon zaben a hukumance.