Ana Kokarin Kare Kasar Kongo Daga Wata Annobar Ebola

  • Ibrahim Garba

Aikin dakile cutar Ebola

Game da cutar Ebola dai, ga dukkan alamu, bakon da aka raka ya dawo - musamman ma a wuraren da aka fai fama da cutar irinsu kasar Kongo (Congo), inda cutar ta saba barnar gaske. To amma wannan karon su ma hukumomi da jami'an jinya sun ja daga.

Yayin da Janhuriyar Dimokaradiyyar Kongo ke fuskantar babbar annobar cutar Ebola a karo na biyu a wannan shekarar, masu kai daukin gaggawa sun yinkuro don dakile yaduwar cutar. A halin da ake ciki ma, masana na kan jaraba ingancin wani rigakafi a inda cutar ta bullo.

Baya ga wannan hobbasar, kwararru a Janhuriyar ta Dimokaradiyyar Kongo na kan tattara bayanai, wadanda za su taimaka wajen gano hanya mafi inganci ta daukar mataki nan gaba akan bullar Ebola da sauran cututtuka masu yado.

Aikin da su ke yi ya hada da bayyana dalla-dallar yadda cuta irin Ebola ke yado ta wajen bin diddigin inda cutar ta bulla, da shata inda wadanda su ka kamu su ke, da kuma samar da ma’aikatan jinya.

Cikakken fahimtar yanayin wuraren da cuta mai yado irin Ebola kan bullo, sannu a hankali zai kai ga samun hanyoyi mafiya inganci na jinya.