Ana Takaddama Kan Fara Shari'ar Sakamakon Zaben Congo

Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta yi watsi da kiran da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi cewa ta jinkirta bayyana sakamako na karshe, na zaben shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya.

Jamhuriyyar Demokradiyyar Congo ta yi watsi da kiran da Kungiyar Tarayyar Afirka (AU) ta yi cewa ta jinkirta bayyana sakamako na karshe, na zaben Shugaban kasa da aka gudanar a watan jiya.

Kasar ta Congo ta kuma jaddada 'yancin kotun kundin tsarin mulkin kasar wadda tuni ma ta fara sauraren karar da aka daukaka kan sakamakon zaben.

Ana kyautata zaton cewa da safiyar yau Juma’a kotun ta kundin tsarin mulkin kasar za ta yanke hukunci kan bukatar da mutumin da ya zo na biyu, wato Martin Fayulu, ya gabatar ta a sake kidaya kuri'un saboda, a cewarsa, an tabka magudi.

Kungiyar tarayyar Afrika ta AU ta fitar da wata sanarwa jiya alhamis, inda ta ke kiran gwamnatin Congo da ta tsayar da sanar da sakamakon zaben inda ta yi ikrarin cewa tana zargin akwai babbar matsala a zaben.

A ranar Lahadin da ta gabata aka sanar da sakamakon cewa dan jam’iyar adawa Felix Tshisekedi, shi ya lashe zaben, amma Fayulu ya kai kara kotu yana mai cewa bai yarda da sakamakon zaben ba.

Fayulu na zargin cewa shugaban kasar na yanzu Joseph kabila ya hada baki da abokin adawarsa wanda ya lashe zaben.