Ana Takon Saka Akan Sarautar Dogon Dutse.

  • Ladan Ayawa

Attajiri Aliko Dangote yana gaida Sarki Sanusi a fadar gwamnatin Jihar Kano.

Ana ci gaba da cece kuce akan sarautar dogon dutse dake cikin jamhuriyar Niger abinda wasu ke ganin ana son a take musu hakkin su abinda suka ce ba zasu yarda da hakan ba.

Yanzu haka dai rikici ya barke akan cancantar tsayawa takarar masarautar tsibirin dogon dutse dake Jamhuriyar Niger.

Wannan rikicin dai ya samo asali ne sakamakon wani tankade da rairaya da akayi a hukumamce wanda ya fito da jerin sunayen wadanda zasu iya tsayawa takarar wannan masarautar.

Sai dai shugaban al’ummar Arawa sunce sun gano cewa yan al’ummar Gubawa ne kawai aka baiwa wannan damar, abinda yasa suka ce da sake.

Mallam Jibrin Baare mai kare muradun Arawa a wannan takaddamar yayi wa wakilin sashen Hausa Sule Mummuni Barma bayanin matsayar da suka cimmawa akan wannan batun.

Ga Sule Mummuni Barma da Karin bayani

Your browser doesn’t support HTML5

Ana Takon Saka Akan Sarautar Dogon Dutse. 2'49