Anambra: Ra'ayoyi Kan Soke Zaben Sanatoci

Masu sauraren kara a wata kotun Najeriya

Ana ta suka tare da yaba matakin soke zabuka da kotun koli ta dauka kan zabukan wasu sanatoci biyu daga jihar Anambra.

Bayan da kotun koli a Najeriya ta soke zabukan wasu ‘yan majalisar dattawa guda biyu daga jihar Anambra da ke kudu maso gabashin kasar, jama'ar yankin suna ta tofa albarkacin bakinsu.

Wadanda lamarin ya shafa sun hada da Mista Andy Uba da ke wakiltar mazabar Anambra ta Kudu, sai kuma Mrs Stella Odua, tsohuwar ministar sufurin jiragen saman Najeriya.

Dukkaninsu a karkashin jam’iyar adawa ta PDP suka ci zabe a matsayin sanatoci.

Yanzu haka kotun ta ba da umurnin a sake wani zabe a yankunan da suka fito.

An dai samu rarrabuwar kawuna kan irin tsokacin da wasu daga cikin al’umar yankin suka yi, yayin da wasu ke sukar matsayar kotun wasu kuwa cewa suke sambarka.

Ga kadan daga cikin ra’ayoyin mutanen jihar ta Anambra kamar yadda wakilin Muryar Amurka Lamido Abubakar Sokoto ya tattaro mana:

Your browser doesn’t support HTML5

Anambra: Ra'ayoyi Kan Soke Zaben sanatoci- 1'14"