Anyi Hasarar Dukiya Mai Tarin Yawa Sakamakon Ambaliya A Jihar Benue.

  • Ladan Ayawa

Hotun ambaliyar ruwa a Jihar Bauci, wadanda aka dauka Alhamis 15 ga Agusta.

Anyi hasarar dukiya mai tarin yawa a jihar Benue sakamakon ambaliyar da akayi, kuma ya shafi kananan hukumomi har 12.

Hukumar bada agajin gaggawa ta Nigeria da ake kira da turanci NEMA, tace ambaliyar ruwa da ya auku a jihar Benue yayi dalilin hasarar dukiya ta miliyoyin kudi, yayinda kuma Jamaa da dama suka kaurace wa muhallan su.

Darektan Hukumar Bada Agajin Gaggawa na kasa Injiniya Mustafa Yunusa Mai Haja ya shaidawa wakiliyar Sashen Hausa na Muryar Amurka Zainab Babaji cewa kananan hukumomi 12 ne wannan balai’n ya shafa a jihar ta Benue.

Yace ambaliyar aba ce da ta tayar da hankalin jamaa musammam mazauna babban birnin jihar wato Makurdi.

Darektan na NEMA ya ziyarci wasu daga wuraren da abin ya faru kuma ya gane wa idanun sa irin barnar da wannan ambaliyar ta haifar.

Injiniya Mustafa yace yanzu haka gwamnatin jihar ta samar da matsagunni ga wadanda wannan abu ya shafa.

Ga Zainab Babaji da karin bayani: 3’20

Your browser doesn’t support HTML5

Anyi hasarar dukiya mai tarin yawa sakamakon ambaliya a jihar Benue.3'20