Anyi Taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Amma Babu Guda Daga Jam'iyyar PDP da Ya Halarci Taron

Ahmed Bola Tinubu daya daga cikin jiga-jigan jam'iyyar APC.

Da yake magana kan taron, gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakarda wamako, yace sun tattauna kan makomarsu bayan sun kammala wa'adi da kuma samarwa jama'a ayyukan yi.
Jiya Jumma'a kungyar gwamnonin Najeriya karkashin jagorncin gwamnan jihar Rivers Chibuke Rotimi Ameach, i ta kammala taronta na bayan bayan nan a Patakwal babban birnin jihar.

Duka gwamnonin dake karkashin jam'iyyar hamayya ta APC su 11 sun halarci taron, amma babu wani takwaran aikinsu daga jam'iyyar PDP ko daya da ya halarci taron.

A cikin batutuwa da gwamnonin suka tattauna harda irin ayyukanda zasu sa gaba bayan sun kammala wa'adin aikinsu da hanyoynda zasu bi domin samarwa jama'a ayyukan yi, da kiwon lafiya da sauransu.

Gwamnan jihar Sokoto Aliyu Magatakarda wamako, wand a yayi magana da wakilin Sashen Hausa Lamido Abubakar yace kungiyar ta kuma duba irin ayyukan canji da jam'iyyar zata saka a gaba da zarar ta kafa gwamnati a tarayya.

Ga karin bayanai.

Your browser doesn’t support HTML5

Anyi Taron Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Amma Babu Guda Daga Jam'iyyar PDP da Ya Halarci Taro - 3'31"