APC Ta Lashe Zaben Kananan Hukumomin Yobe

APC

Shugaban hukumar zabe mai zaman kanta ta jihar Yobe, ya bayyana sakamakon zaben kananan hukumomi da aka gudanar na ranar Asabar a jihar.

Alhaji Mohammed Joro Abdu, shine ya bayyana sakamakon zaben ga manema labarai, inda yace jam’iyyar APC ce ta samu nasarar lashe zaben dukkanin kujerun kananan hukumomi 17 dake fadin jihar.

Wannan dai shine karo na uku da jihar Yobe ke gudanar da zaben kananan hukumomi karkashin jagorancin gwamnan jihar Alhaji Ibrahim Gaidam, tun hawansa karagar mulki a jihar.

Sai dai kuma wannan sakamako yazowa mutane da mamaki ganin cewa baki ‘daya shugabannin kananan hukumomin guda 17 ‘ya ‘yan jam’iyya mai mulki ne a jihar, APC, kuma babu wani abokin hamayya a jihar da ya kalubalanci zaben.

Domin karin bayani saurari rahotan Haruna Dauda.

Your browser doesn’t support HTML5

APC Ta Lashe Dukkan Zaben Shugabannin Kananan Hukumomin Jihar Yobe - 3'27"