Atiku Ya Yi Allah Wadai Da Yunkurin Juyin Mulki a Habasha

Atiku Abubakar

Tsohon mataimakin shugaban Najeriya, kuma dan takarar shugaban kasa a zaben 2019 karkashin jam’iyyar adawa ta PDP, Atiku Abubakar, ya yi Allah wadai da yunkurin da wasu sojoji suka yi na kifar da “zababbiyar gwamnatin Habasha.”

Atiku ya bayyana hakan ne a shafinsa na Twitter a yau Lahadi, inda ya kara da cewa, mulkin dimokradiyya ya zama dawwamamme a nahiyar Afirka.

“Yunkurin juyin mulkin da aka yi na kifar da zababbiyar gwamnati ta dimokradiyya, abbin Allah wadai ne.”

Ya kara da cewa, “mulkin dimokradiyya ya zama dawwamamme a nahiyar Afirka, a matsayina na mai rajin kare mulkin dimokradiyya, ina mai mika hannaye na dama domin nuna goyon bayana ga jama’ar Ethiopia – Allah ya ja zamanin mulkin dimokradiyya a Afirka.”

A yau Lahadi Jami’ai a Ethiopia, suka ce mai tsaron lafiyar shugaban rundunar dakarun kasa na kasar ta Habasha ya harbe shi har lahira, sa’o’i bayan da jami’ai suka ce an yi yunkurin juyin mulki a jihar Amhara.

Mai magana da yawaun Firai Ministan Habasha, Abiy Ahmed, ta ce an kashe shugaban dakarun Chief Sear Mekonnen da wani janar mai ritaya a wasu hare-hare da aka kai a gidan Sear.

Kafafen yada labaran kasar sun ruwaito cewa, shugaban jam’ian tsaron jihar ta Amhara, Janar Asamnew Tsige ne ya jagoranci yunkurin na juyin mulki.

Bayanai sun yi nuni da cewa, tuni an kama mai tsaron lafiyar da ya kashe shugaban dakarun kasar, amma har yanzu ba a ga Janar Asamnew ba.