AU Ta Yi Kira Ga Sojojin Mali Su Saki Shugaba Keita

Sojojin Mali a birnin Bamako

Kasashe da kungiyoyi, na ci gaba da yin Allah wadai da sauyin gwamnatin da aka yi a kasar Mali ba tare da bin matakan da doka ta shimfida ba inda suka yi kira da a saki shugaban kasar Ibrahim Boubacar Keita da mukarrabansa.

A baya-bayan nan Shugaban kungiyar kasashen Tarayyar Afirka ta AU kana shugaban kasar Afirka ta Kudu Cyril Ramaposa, ya yi tir da kifar da gwamnatin Mali da wasu sojoji suka yi.

Cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Laraba, Ramaposa ya yi kira ga sojojin da suka yi bore a kasar ta Mali da ke yammacin Afirka, da su saki shugaba Ibrahim Boubacar Keita, Firai Minista Boibou Cisse da sauran manyan shugabannin gwamnatin kasar.

A lokacin da yake jawabinsa na yin murabus, Keita, wanda ake tsare da shi a wani sansani da ke kusa da Bamako, babban birnin kasar, ya sanar da rushe majalisar kasar da gwamnatin Firai minister Boubou.

Har izuwa ranar Laraba, Jami’an sojojin da suke kiran kansu kwamitin ceto al’ummah, na ci gaba da rike Keita.

A halin da ake ciki, sojojin sun ce suna kokarin ganin an gudanar da zabe.

Kungiyar kasashen Afrika ta AU ta dakatar da kasar Mali daga cikin kungiyar, har sai an maido da doka da oda tare da sakin manyan jami’an gwamnatin.