Australia Ta Wargaza Wata Markarshiyar Tarwatsa Jirgin Saman Fasinja.

Dansanda yake tsaye a wani titi da aka hana bi, bayan d a suka kama mutane hudu dangane da yunkurin tarwatsa jirgin fasinja.

PM kasar, yace 'Yansanda sun wargaza wata makarkashiyar da 'yan ta'adda suka shirya da nufin tarwatsa jirgin saman fasinja.

PM Australia, yace 'Yansandan kasar sun wargaza wata makarkashiyar da 'yan ta'adda suka shirya da nufin tarwatsa jirgin saman fasinja.

Masu bincike sun ce suna da bayanan cewa shirin tarwatsa jirgin ya kunshi amfani "da nakiyoyi." An kama mutane hudu bayan wani somame da aka kai a fadin birnin Sydney jiya Asabar, da 'Yansanda dauke da makamai da jami'ai daga hukumar leken asirin kasar suka kaddamar.

Wata mace wacce tace mijinta da danta suna daga cikin wadanda aka kama, ta karyata cewa suna da wata dangantaka da masu tsatsatsauran ra'ayi.

Manyan jami'an 'Yansanda suka ce somame da suka kai yana da nasaba da zargin wata makarkashiyar masu "ikirarin Islama", koda shike babu cikakken bayani kan lokaci da wurin da suke shirin kai harin. Rahotanni suka ce 'Yansanda basu shirya kai somamen ba, amma suka dauki matakin bayan da aka kai musu tsegumi.

PM Australia Malcolm Turnbull, yace hukumomi sun wargaza wata makarkashiya da aka tsara sosai.

An dauki karin matakan tsaro a tashar jirgin sama dake Sydney, yanzu an fadada shi a duk fadin kasar.