Ba A Bukatar Karin Shaidu A Shari'ar Tsige Shugaba Trump

Wani dan majalisar dattawan Amurka daga jam’iyyar Republican ya ce babu bukatar a gayyato karin shaidu game da batun shari’ar tsige Shugaba Donald Trump saboda ‘yan Democrat sun riga sun gabatar da hujjojinsu akan Shugaban kuma laifin da suke zargin ya aikata bai kai a tsige shi ba, amma dai “bai dace ba.”

Sanata Lamar Alexander

A wata sanarwa da aka fidda jiya Alhamis, Sanata Lamar Alexander ya bayyana cewa babu bukatar karin hujjoji don tabbatar da abin da aka riga aka tabbatar kuma abin da kundin tsarin mulkin kasar bai bayyana a matsayin laifin da ya cancanci a tsige Shugaba ba. Alexander ya kara da cewa tsarin mulkin kasar bai ba majalisar dattawa ikon tumbuke Shugaban kasa daga mukaminsa ba ko hana shi tsayawa takara a wannan shekarar saboda kawai wasu abubuwa da ya yi da ba su dace ba.

An bukaci ‘yan Republican guda hudu daga majalisar dattawan kasar su hada kai da ‘yan Democrat da sauran wadanda ba sa karkashin wata jam’iyya su 47 a majalisar dokokin don kada kuri’a akan ba wasu shaidu dama su bada ba’asi a shari’ar tsige Trump.