Shugaba Muhammadu Buhari Yace Ba Zai Lamunta da Masu Neman Raba Najeriya Ba.

ABUJA: Shugaba Buhari.

Shugaban ya bayyana haka ne cikin jawabinsa na cikar Najeriya shekaru 57 da samun 'yancin kai.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari yace ko kusa gwamnatinsa ba zata kyale a raba Najeriya ba.

Shugaba Muhammadu Buhari wand a ya bayyana haka a cikin jawabinsa na murnar cikar kasar shekaru 57 da samun 'yancin kai, yace manya a yankin kudu maso gabashin Najeriya sun yi sake da basu ja kunnen matasa da suke kan gaba kan neman kafa kasar Biafra ba. Yace galibin masu neman kafa kasar Biafra a halin yanzu ba'a ma haife su ba a lokacin da aka yi yakin.

Shugaba Buhari yace a matsayinsa na tsohon soja, wanda ya bada tasa gudumawa wajen tabbatar da hadin kan kasar ba zai amince da wadanda suke ta gwagawar neman sake tada fitina ba, domin basu san irin rayuka da dukiya da suka salwanta a lokacin yakin basasar ba.

Shugaban ya kuma yi magana kan yaki da cin hanci da rashawa da kuma kokarin gwamnatinsa na samar da ayyukan yi ga matasa.

Ga karin bayani.

Your browser doesn’t support HTML5

Jawabin shugaba Buhari