Ba Zan Koma Kungiyar Gwamnoni Ba Sai An Bayyana Gaskiyar Matsayinmu-Isa Yuguda

Shugaban Kasar Najeriya Goodluck Jonathan yana gabatar da rahoton aikin da gwamnatinsa ta gudanar cikin shekaru biyu

Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda yace ba zai koma kungiyar gwamnoni ba sai an fayyacewa 'yan Najeriya gaskiyar matsayin gwamnonin arewacin kasar kan zaben shugaban kungiyar gwamnoni
Gwamnan jihar Bauchi Isa Yuguda ya bayyana dalilinsa na janye jiki daga kungiyar gwamnonin kasar.

A cikin hirarshi da manema labarai gwamna Yuguda ya bayyana cewa, gwamnonin arewacin Najeriya goma sha tara sun amince su tsaida gwamnan jihar Plateau Jonah Jang a matsayin wanda zai gaji gwamna Rotimi Amechi na jihar Rivers a matsayin shugaban kungiyar gwamnonin.

Bisa ga cewar gwamna Yuguda, tsarin kungiyar bai bada damar shugabantar kungiyar karo na biyu ba. Ya bayyana cewa, hakin shugaban kungiyar gwamnonin arewacin Najeriya ne, ya fita fili ya fayyacewa ‘yan Najeriya gaskiyar matsayinsu a kan wanda suka tsayar ya wakilcesu ba tare da hamayya ba, abinda yace ya basu damar tsaida shugaba sabili da sune suke da rinjaye.

Da yake amsa tambayoyin wakilinmu Abdulwahab Mohammed, gwamna Isa Yuguda, yace hakin al’ummar jihar da suka zabe shi yasa ya zama tilas ya tsaya kan gaskiya domin kare mutumcinsu.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira da Gwamnan Jihar Bauchi Isa Yuguda Kan zaben kungiyar gwamnoni-3:34