Ba’a Soki Wasikata ba – inji Nyako

Admiral Murtala Nyako mai ritaya, gwamnan Jihar Adamawa.

A karon farko gwamnan Jihar Adamawa Murtala Nyako, ya musanta bayanan da wasu gwamnoni suka yi, na cewa a taron majalisar tsaro da aka yi a ranar Alhamis taron ya soki wasikar da ya rubutawa gwamnonin arewa.
Gwamnan Adamawan da yake ganawa da manema labarai a birnin Yola, jim kadan da komowarsa gida, yace yayi mamaki da ake cewa wai taron yayi Allah wadai da wasikar daya rubutan, Murtala Nyako yace ba haka zancen yake ba,domin a cewarsa ya rubuta wasikar ne da kyakkyawar manufa na an karar da shugabanin kasar game da abubuwan dake faruwa.

Murtala Nyako yace “akan me za’a soke ni? Abinda yafi musu alheri shine su kama bakinsu suyi shiru kurum. Don kasan babu yadda za’a yi inyi wannan magana, magana na babatu. Saboda haka a batta kurum.”

A kwanakin baya gwamnan Jihar ta Adamawa, daya daga cikin jihohi uku dake da dokar-ta-baci, Nyako ya dauki alwashin tattara takardun shaidu domin kai karar shugaban Najeriya a kotun bin kadin manyan laifuka ta kasa da kasa, wato ICC a takaice dake can birnin Hague a Netherlands.

A halin yanzu dai gwamnatin tarayya ta rage yawan jami’an tsaro dake gadin gwamnan Jihar Adamawan daga 120 zuwa 30 kacal, wanda kawo yanzu babu cikakken bayani daga hukumomin abinda ya shafa, yayin da jiragen sama masu saukar ungulu na soji ke cigaba da shawagi.

Your browser doesn’t support HTML5

Martani Akan Kalaman Nyako - 3'45"