Babu Dalilin Kama Omar Al-Bashir A Najeriya: Hassan Tukur

Shugabannin kasashen cikin kungiyar Tarayyar Afirka a wurin taron

Ambasada Hassan Tukur, babban jami'i a ofishin shugaban Najeriya yace shugaban kasar Sudan Omar Al-Bashir yaje Najeriya ne bisa gayyatar Kungiyar hadin kan Afrika
A daidai lokacin da shugabannin kasashen nahiyar Afrika ke halartar wani kasaitaccen taro a babban birnin tarayya Abuja, da zumar yaki da cututukan tarin fuka da kamjamau da kuma zazazabin cizon sauro, hankalin wadansu ‘yan gwaggwarmaya ya koma kan batun sammacen da kotun duniya ta bayar na kama shugaban kasar Sudan Omar al-Bashir.

Kungiyar kare hakkin bil’adama ta Human Right Watch da kuma wata kungiya mai suna Kungiyar kawancen masu goyon bayan kutun duniya ta Najeriya, sun garzaya kotu domin neman ta tilastawa gwamnatin tarayya umarta kama shugaba Omar Al-bashir.

A cikin hirarsu da wakilinmu Umar Faruk Musa, wani babban jami’i a ofishin shugaban kasa, jakade Hassan Tukur ya bayyana cewa, shugaban kasar Mali yaje Najeriya ne bisa gayyata da kuma amincewar kungiyar hadin kan Afirka wadda ta goyi bayan wofinta sammacen na kotun duniya, sabili da haka babu dalilin da zai sa Najeriya ta bada umarnin kama shi.

Your browser doesn’t support HTML5

Hira Da Jakade Hassan Tukuru Kan Batun Kama Omar Al-Bashir. 3:10