Babban Bankin Najeriya ko CBN Ya Horas da 'Yan Gudun Hijira

Wasu 'yan gudun hijira

A karon farko babban bankin Najeriya ya gudanar da horas da 'yangudun hijira da 'yan Boko Haram suka rabasu da muhallansu.

Manufar horaswar ita ce zaburar dasu ta fuskar harkokin sana'a yadda zasu dogara da kansu inda suka koma garuruwansu da yanzu an samu an kwatosu daga hannun 'yan Boko Haram.

'Yan gudun hijiran da suka samu horaswar sun zanta da Muryar Amurka. Wani daga Michika yace abubuwan da basu sani ba an koya masu kamar tanadi musamman kudi da sana'o'i. Yace yanzu da 'yan kalilan kudinsa ya san yadda zai gudanar da harakar kasuwanci.

Cikin abubuwan da aka koya masu har da kiwo da kula da yanayin kasuwa. To saidai wai suna bukatar taimakon gwamnati domin su kafa nasu fannonin kasuwanci.

Abin da yawancinsu suka fi nanatawa an koya masu shi ne tanadin arziki, wato kaucewa almubazaranci.

Ga cikakken bayani na Ibrahim Abdulaziz.

Your browser doesn’t support HTML5

Babban Bankin Najeriya ko CBN Ya Horas da 'Yan Gudun Hijira Kasuwanci - 3' 53"